A jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwararsa ta kasar Switzerland madam Doris Leuthard suka gana da wakilan sashen tattalin arzikin Switzerland a birnin Bern, hedkwatar kasar.
A jawabinsa, shugaba Xi ya yi karin haske game da halin tattalin arzikin kasarsa, inda ya jaddada cewa, kasar Sin ba za ta iya samun ci gaba ita kadai ba, sai da taimakon sauran kasashen duniya, kana kuma ba za a samu wadatuwa a duniya ba, sai kasar Sin ta bunkasa. Kasar Sin tana da imanin samun bunkasuwar tattalin arziki ba tare da tangarda ba, kuma tana kara kawo wa jama'arta alheri, yayin da take ba da taimako wajen farfado da tattalin arzikin duniya, tare da kara samar da zarafi ga sauran kasashen duniya, ciki had da kasar ta Switzerland. (Tasallah Yuan)