in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)Xi Jinping ya halarci bikin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na 2017
2017-01-17 20:35:30 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bikin bude taron shekara-shekara, na dandalin tattauna batutuwan tattalin arzikin duniya na 2017 a birnin Davos dake kasar Switzerland da sanyin safiyar yau Talata inda kuma ya gabatar da jawabi.

Wannan ne dai karo na farko da shugaban kasar ta Sin ya halarci taron shekara-shekarar na dandalin tattaunawar.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, maida tsarin bai daya na tattalin arzikin duniya, a matsayin dalilin da ya sa aka samu matsalolin duniya bai dace da yanayin duniya ba, kana hakan ba zai iya warware matsaloli ba.

Ya ce a halin yanzu, dalilin da ya sa aka samu raguwar tattalin arzikin duniya cikin dogon lokaci shi ne, rashin karfin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da rashin kulawa a fannin tattalin arzikin duniya, da kuma rashin samun daidaito kan ci gaban tattalin arzikin duniya.

Shugaba Xi ya ce bunkasuwar Sin ta kasance wata dama ga duniya, duba da cewa ta na samar da moriya, kana ta samar da gudummawa ga raya tsarin bai daya na tattalin arzikin duniya.

Ana sa ran cewa, a shekaru 5 masu zuwa, Sin za ta shigar da kayayaki da yawansu zai kai dala biliyan 8000 cikin kasuwannin duniya, kuma yawan jarin da ta zuba ga kasashen waje zai kai dala biliyan 750, kuma yawan Sinawa dake zuwa yawon shakatawa a kasashen waje zai kai miliyan 700. Kana game da bangaren ciniki da masana'antu, bunkasuwar Sin ta kasance wata kyakkyawar dama.

A cikin shekaru fiye da 3, tun bayan da aka gabatar da kira ga shirin nan na "ziri daya da hanya daya", kasashe da hukumomin duniya fiye da 100 sun amsa kiran, kana fiye da 40 a cikinsu sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa tare da kasar Sin, in ji shugaban kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China