A jiya Litinin ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da shugabannin majalisar wakilan da na dattawan Switzerland kasar, a birnin Bern, hedkwatar kasar.
A yayin ganawar, shugaban kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin na son hada kai da kasar Switzerland wajen inganta hadin gwiwa a al'amuran kasa da kasa, kara kyautata huldar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare da ke shafar kirkire-kirkire, a kokarin raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 zuwa sabon mataki. (Tasallah Yuan)