in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban dandalin tatttaunawar tattalin arzikin duniya
2017-01-18 09:39:41 cri

Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya Mista Klaus Schwab a birnin Davos na kasar Switzerland.

Xi Jinping ya jaddada cewa, taken taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na wannan shekara, ya dace da halin da ake ciki yanzu a fadin duniya, wanda ya samarwa duniya mafita daga halin kuncin da ake ciki. Xi ya yi kira da a bada kwarin-gwiwa ga kokarin da ake yi na dunkulewar tattalin arzikin duniya waje daya.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, kasar Sin na fadada hadin-gwiwa tare da dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya, kuma an cimma nasarori da dama. Haka kuma kasar Sin ta taba karbar bakuncin dandalin Davos na lokacin zafi har sau goma a tarihi, wanda ya kara taka muhimmiyar rawa a fadin duniya.

A waje guda, Mista Klaus Schwab ya sake godewa shugaban Sin Xi Jinping saboda muhimmin jawabi mai fadakarwa da ya gabatar. Klaus Schwab ya ce, jawabin Xi ya nuna alkibla ga ci gaban tattalin arzikin duniya a nan gaba, kuma kasar Sin ta dade tana nuna cikakken goyon-baya ga wannan dandali. Dandalin tattaunawar yana fatan inganta alakar abokantaka tare da kasar Sin, a kokarin da ake na warware matsalolin da duniya ke fuskanta.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China