Yayin ganawar ta su, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce, kasar Sin tana goyon bayan wasannin Olympics, gami da kokarin halartar wasannin. kuma birnin Beijing na kasar Sin shi ne birni daya tak a duniya, da ta taba karbar bakuncin wasannin Olympics na lokacin zafi, zai kuma zama mai masaukin baki ga wasannin Olympics na lokacin sanyi. A cewar shugaban na Sin wannan wata gudunmowa ce da Sin ta samar ga ayyukan wasannin Olympics.
A nasa jawabin, Tomas Bach ya ce, kwamitin IOC yana lura da aikin gyare-gyare, da ci gaban tattalin arziki na kasar Sin. Haka kuma yana da imanin cewa, kasar za ta samu takamaiman ci gaba a fannonin siyasa, tattalin arziki, al'adu, wasannin motsa jiki, da dai makamantansu.
Sabili da haka, kwamitin IOC na fatan ci gaba da kokari tare da kwamitin shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi a Beijing, domin tabbatar da nasarar aikin share fagen babban bikin gasar yadda ya kamata, ta yadda za a samu ganin wasannin gasar Olympics masu kayatarwa a birnin na Beijing a shekarar 2022.(Bello Wang)