in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da kusoshin MDD
2017-01-19 09:07:46 cri

A jiya Laraba ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da Peter Thomson, shugaban babban taron MDD karo na 71 da Antonio Guterres, babban sakataren MDD, inda ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bin manufar kulla hulda da sassa daban daban. Haka kuma Sin za ta kare martaba kundin tsarin MDD da ka'idojinta, tare da mara wa MDD baya ta yadda za ta kara taka rawa a ayyukan kiyaye zaman lafiya a duniya da kara kokarin samun ci gaba tare.

Shugaban Sin ya kara da cewa, MDD, wata kungiya ce mai martaba da aka kafa tsakanin gwamnatocin kasa da kasa, wadda kuma take wakiltar kasashen duniya. Don haka ya kamata MDD ta taka muhimmiyar rawa wajen daidaita harkokin kasa da kasa.

A nasu bangaren kuma, Peter Thomson da Antonio Guterres sun bayyana cewa, a yayin taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya da ya gudana a jiya, shugaba Xi ya sake nanata manufar kasar Sin ta ci gaba da kulla hulda a tsakanin kasa kasa, lamarin da ya samu yabo sosai a duniya, kuma wannan wani muhimmin tabbaci ne ga MDD da ma harkokin kulla hulda a tsakanin kasa da kasa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China