in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban kasar Sin a babban zauren MDD za ta karfafa gwiwar mutane, in ji kakakin MDD
2017-01-17 12:41:56 cri

Kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq ya ce, ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ofishin MDD dake Geneva a nan gaba kadan, za ta karfafa gwiwar jama'a sosai.

A yayin da yake amsa tambayar manema labaru a gun taron manema labaru da aka saba shiryawa a babban zauren MDD a New York, mista Haq ya nuna cewa, ziyarar da shugaba Xi zai kai ofihin MDD dake birnin Geneva, ziyara ce mai muhimmiya da shugaban kasar ta Sin zai kai, lamarin da ya karfafa gwiwar mutane sosai. Ana saran babban sakataren MDD António Guterres zai gana da shugaba Xi, inda za su tattauna wasu al'amuran da ke jawo hankalinsu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China