in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya kai ziyara hedkwatar WHO
2017-01-19 09:13:06 cri

A jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara hedkwatar hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO da ke birnin Geneva, inda ya gana da babbar darektar hukumar, Madam Margaret Chan.

A ganawar tasu, Mr. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, bunkasa harkokin kiwon lafiya wani muhimmin mataki ne na tabbatar da shirin samun dauwamammen ci gaba a duniya nan da shekarar 2030, yana mai cewa, Kasar Sin ta kafa tsarin inshorar lafiya mafi girma a duniya, kuma tana maraba da taimakon hukumar WHO wajen kara bunkasa harkokin kiwon lafiya.
Mr. Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana son hada gwiwa da WHO, a fannonin da suka hada da tabbatar da shirin samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 da kuma bada gudunmawa ga kasashe masu tasowa.

A nata bangare, Madam Margaret Chan ta ce, kasar Sin na daga cikin kasashen da suka kafa hukumar WHO, a don haka, WHO za ta tsaya tsayin daka a kan manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Hukumar WHO ta kuma yabawa kasar Sin kan kwarewarta wajen jagorantar harkokin kiwon lafiya a duniya, tana mai fatan karfafa hadin gwiwa da ita bisa tsarin "ziri daya da hanya daya", don inganta harkokin kiwon lafiya a kasashen da tsarin ya shafa.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China