in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunawa da 'yan wasan da muka yi rashinsu a 2016
2017-01-05 20:49:09 cri

Daga karshe za mu yi bayani kan Craig Sager, sanannen mai rubuta rahoton wasannin NBA, wato shahararren tsarin gasar wasan kwallon kwando na kasar Amurka, wanda ya rasu a ranar 15 ga watan Disamba yana da shekaru 65 a duniya. Ya kasance daya daga cikin fitattun 'yan jarida na kafar yada labaru ta Turner broadcasting network. Sager ya kuma yi fice a matsayinsa na mai fafutukar yaki da cutar data shafi sankarar jini tun lokacin da aka tabbatar masa ya kamu da cutar a shekarar 2014.

Ya shahara sosai game da irin yadda yake yin kwalliya ya fito tsab, lamarin da ke bashi kwarin gwiwa yayin gabatar da labarai da dumi duminsu daga gefen filin wasa, a sama da shekaru 40 da ya shafe a wannan sana'a.

Bayan rasuwar Craig, kwamishin NBA Adam Silver ya ba da sanarwa cewa, "a madadina da dukkan iyalan NBA, muna nuna alhini game da rasuwar Craig Sager. Craig yana da muhimmanci a NBA kamar yadda 'yan wasa da kociyan NBA suke da shi." A cewar Silver.(Ahmad/Saminu)


1 2 3 4 5 6 7 8 9
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China