in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bruce Lee da wasan Jeet Kune Do
2016-12-01 12:59:44 cri


An haifi Bruce Lee a shekarar 1940 a San Francisco na kasar Amurka, amma kauyensa na asali shi ne wajen garin Shende dake jihar Guangdong na kasar Sin. Ya shahara dalilin yadda ya yi kokarin gadon fasahar wasan Kunfu na kasar Sin, da nazarinta, gami da koyon fasahar sauran wasannin Kunfu na kasashe daban daban don kirkiro wasan irin musamman na kansa, wato Jeet Kune Do.

Haka kuma ya yada fasahar Kunfu na kasar Sin zuwa wurare daban daban, bisa fina-finan da ya dauka ya kuma kasance jarumi ciki, wadanda suka samu karbuwa sosai, tare da farin jini har zuwa yanzu.

Don takaita tarihin Bruce Lee, ma iya cewa akwai manyan bangarori 2 da ya fi mai da hankali a kai, wato wasan Kunfu da kuma daukar Fim. A bangare na biyu, hakika ya fara nuna kwarewa tun yana karami. A shekarar 1941, lokacin da Bruce yake da watanni 3 a duniya, ya riga ya fara nuna fuskarsa a wani fim da aka dauka mai taken "Golden Gate Girl", wato "matar Golden Gate" a Hausance.

Dalilin da ya sa Burce Lee ya fara jibantar aikin daukar fim da wuri shi ne domin babansa Lee Haiquan ya kasance wani shahararren dan wasan kwaikwayon gargarjiyar kasar Sin, wanda ya yi gudun hijira tare da iyalinsa zuwa kasar Amurka a shekarar 1940 domin gudun harin da sojojin Japan suka kai ma kasar Sin. Sa'an nan a shekarar 1941, wato bayan haifuwar Bruce, LEE-HOI-CHUEN ya yi niyyar koma birnin Hongkong, ganin a can ya fi sauki wajen gudanar da aikinsa.

Da yawa daga cikin 'yan wasan kwaikwayon gargajiyar kasar Sin suna da fasahar Kunfu domin aikinsu ya kan bukace su nuna Kunfu a kan dandali. Don haka LEE-HOI-CHUEN shi ma ya kware wajen Kunfu, abin da ya sa ya fara koyar da fasahar wasan Taichi ga Bruce Lee tun yana da shekaru 7 a duniya.

Masu sauraro da suka saurari bayanin da muka gabatar dagane da wasan Taichi na kasar Sin, za su san cewa wasan a kan yi shi sannu a hankali, ba kamar sauran wasannin Kunfu ba. Dalilin da ya sa LEE-HOI-CHUEN ya koyar da dansa fasahar wasan Taichi, shi ne domin neman sanya shi samun karfin jiki, tare da daidaita halayyarsa, don mai da shi ya zama wani yaro mai natsuwa. Sai dai yunkurin LEE-HOI-CHUEN na daidaita halayyar dansa bai yi amfani sosai ba, domin Bruce ya kasance wani yaro mai son fada. A lokacin, yayin da iyalan Bruce Lee suke cin abinci tare, a kan ji wani amon 'Kn Kn Kn' mai ban mamaki, sai aka dubi inda dalilin muryar yake, an ga ashe shi Bruce Lee yana cin abinci yana buga kujera da hannu. An tambaye shi dalilin da ya sa ya yi haka, sai ya amsa cewa, mutane da yawa suna son fada da shi, don haka yana son horar da hannunsa don ya zama mai tauri.

Irin halayyarsa ya sa yaron ya fara bukatar koyon fasahar fada. Zuwa shekarar 1954 yayin da Bruce yake da shekaru 13 a duniya, ya je wajen shahararren malamai mai koyar da fasahar Kunfu Ip Man, don koyon fasahar wasan WingTsun. Fasahar nan tana bukatar a yi motsi kadan tare da fitar da babban karfi, don dacewa da yanayin fada tsakanin mutane yayin da suke kusa da juna. Bruce ya koyi wasan WingTsun, ya kuma ari fasaharsa wajen kirkiro wasan na kansa wato Jeet Kune Do.

Sauran mutanen da Bruce Lee ya taba koyon fasaharsu sun hada da JHOON-GOO-RHEE, dan asalin kasar Koriya, kuma kwararren malami mai koyar da wasan Taekwondo a kasar Amurka, da Ed Parker, wanda ya fara yada wasan Karate na kasar Japan zuwa kasar Amurka, da GENE-LEBLL, wanda ya yada wasan Judo a kasar Amurka. Ta haka, za mu iya gane cewa, Bruce Lee ya yi kokarin nazarin wasannin fada na kasashe daban daban, don samun fasahohi masu ci gaba wadanda ke da amfani, sa'an nan ya sanya su cikin fasaharsa. Dalilin hakan ya sa Bruce ya kirkiro Kunfu mai karfi matuka.

A shekarar 1959, yayin da yake da shekaru 18 a duniya, Bruce Lee ya tafi kasar Amurka don karatu, inda a cikin jami'a ya fara kafa wurin koyar da wasan Kunfu. Jami'ar da ta shiga ita ce Jami'ar Washington ta birnin Seattle, inda ya koyi fasahar wasan kwaikwayo.

A shekarar 1967, lokacin da Bruce Lee yake da shekaru 27 a duniya, ya kafa wasan Kunfu iri na kansa, wanda ke da taken "Jeet Kune Do", a kasar Amurka. Ya kafa wasan ne bisa hada fasahohin fada na wurare daban daban a waje guda. Ma'anar "Jeet Kune Do" ita ce "dabarar katse bugun da aka yi maka", wanda ya bukaci a yi fada cikin 'yanci maimakon tsaya kan wani salon fada.

Yayin da yake kirkiro fasahar wasan "Jeet Kune Do", Bruce ya yi amfani da wasu tunani masu zurfi na kasar Sin, wadanda suka shafi ma'anar " Akwai" da " Babu". Bruce ya ce duk da cewa babu tsayayyen motsi ko kuma wani salo na musamman cikin wasan da ya tsara ba, amma ana iya amfani da fasaharsa don tinkarar fasahohin fada nau'o'i daban daban. Fasaharsa ita ce wata hanya da ake bi wajen horar da wani makami da ko wane mutum ke da shi, wato jiki.

Wani fasaha mai muhimmanci da wasan "Jeet Kune Do" da Bruce Lee ya tsara ya kunsa, ita ce fasahar "Cun Quan", wato yadda ake buga da karfi amma yayin da ake zama kurkusa da abin da aka buga. Fasahar nan ita ce abun da Bruce ya yi aro daga wasan Kunfu na "Win Tsun" na kasar Sin, domin da ma ya taba koyon wasan " Win Tsun" a wajen Ip Man.

Idan wani mutum yana son buga wani, za mu ga yadda ya janye hannunsa da farko, sa'an nan ya mika shi cikin sauri don samar da cikakken karfi. Sai dai lokacin da abokin gabansa ya ga mutumin ya janye hannunsa, ya san zai buga da hannun ke nan, kuma zai shirya. Amma idan mutum ya san fasahar "Cun Quan", to, ba ya bukatar janye hannu da farko, kai tsaye zai mika hannu. Duk lokacin da hannun mutum ya zama kusa da jikin abokin gaba, to, zai zama mai saurin gaske tare da samar da karfi matuka. Ta hakan, ba za a samu damar zama cikin shiri don tsaron kai ba.

Ban da Jeet Kune Do, Bruce Lee ya kware wajen amfani da wani sandar musamman mai suna "Shuang Jie Gun". Sandar nan tana da kashi 2, kuma an hada wani bangare nasu da sarka. Ta wannan tsari, sandar za a iya buga da ita, kuma za a iya amfani da ita kamar bulala. Sai dai wasa da sandar na da wuya, domin idan ba a kware ba, a kan iya lahanta kai, maimakon kai hari ga abokin gaba.

Bruce Lee ya samu kwarewa kan wasan sandar ne, ta hanyar gwada fasaharta tare da shahararen malami mai koyar da fasahar wasan sanda dan kasar Philippines Dan Inosanto. Kuma ya fara nuna fasaharsa cikin jerin wasannin kwaikwayo na The Green Hornet da aka nuna a shekarar 1966, inda ya yi kwaikwayon wani jarumi na biyu, wanda ke kokarin tallafawa jarumi wajen yakar miyagun kwayoyi. Daga bisani, a cikin wasu fina-finai, Bruce ya fara nuna fasahar yon amfani da sandar "Shuang Jie Gun" guda 2 a lokaci daya, wato yana rike sandar guda a ko wane hannunsa yana wasa da su.

Kallon yadda Bruce Lee ke amfani da sandar, da yadda makamin yana da karfi sosai, ya sa samarin Amurka da yawa su ma sun fara koyon fasaharta. Sai dai wuyar amfani da sanda ya kan sa aka lahanta wani, ko kuma wanda ke amfani da sandar shi kansa. Saboda haka wasu jihohin kasar sun sanar da dokar hana rike ko kuma amfani da sandar "Shuang Jie Gun".

Halayyar Bruce Lee ta sa shi sannanne a cikin al'umma, duk inda yake zama. Domin yana kaunar wasan Kunfu, kuma yana son gwada fasahar Kunfu tare da masu kwarewar wasan na wurare daban daban, tare da koyon fasahar ci gaba. Ban da haka kuma, a kasar Amurka ya zama wani dan wasan kwaikwayo, wanda ya kasance jarumi a cikin fina-finan da aka dauka daban daban, kuma a cikinsu ya yi kokarin nuna fasaharsa wajen wasan Kunfu. Fina-finansa sun samu karbuwa sosai, wadanda suka taimaka wajen sanya fasahar Kunfu ta yi farin jini a duk duniya.

Kwarewar Bruce Lee a fannin wasan Kunfu ya sa aka yi nazari a kan jikinsa, a kuma rubuta bayani dangane da nazarin. Bayanin ya ce Bruce Lee zai iya tsalle tare da shura wani fitila wanda tsayinsa ya kai kimanin mita 2.5. Haka kuma karfin bugunsa da sanda mai kashi 2 ya kai laba 1600. An ce idan ya harba kafa zuwa wani gefe zai iya lalata wata jaka mai rairayi, wanda nauyinsa ya kai kilo 45. Ban da haka kuma bugun da ya yi da hannu, nauyinsa ya kai kilo 400, wanda ya yi daidai da na sarkin dambe Muhammad Ali. Ko da yake nauyin jikin Ali ya kai laba 260, yayin da nauyin Bruce Lee laba 130 da wani abu kawai.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China