To, ban da wannan kuma,wani dan wasan da za a dade ana jimamin rabuwa da shi, shi ne Liu Lianman dan asalin kasar Sin, wanda shi ma ya rasu a shekarar 2016 yana da shekaru 83. Liu wanda ya shahara a wasan hawa tsaunuka, ya rasu ne a ranar 27 ga watan Afirilu a lardin Harbin dake arewacin kasar Sin.
Duk da cewa ba dan wasa ne da duniya ta san shi sosai ba, amma halayyar sa ta kyautatawa jama'a, ta sanya shi samun karbuwa a dukkanin fadin kasar Sin. Mr. Liu wanda ya taba zama mamba a tawagar 'yan wasan kasar Sin masu hawa tsaunuka, shekaru 57 da suka gabata ya taba hawa tsaunin Qomolangma,wanda shi ne tsauni mafi tsayi a duniya. A kuma wannan lokaci ne aka ce ya baiwa abokin hawa tsaunin sa kurtun sa na shakar iska, ya kuma goya shi yayin da yake kokarin haye wani wuri a tsaunin. Sakamakon wannan jarumta da ya nuna, a karon farko a tarihin bil adama, Liu da abokin hawa tsaunin sa suka cimma nasarar kammala hawa wannan tsauni, ta bangare mafi tsawo a kusurwar arewa.
Masharhanta da dama na ganin za a dade ana tunawa da Liu a fagen wasanni, bisa kyawun halin sa, da jarumtar da ya nuna a lokacin rayuwar sa.