in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zakaran wasan Olympic zai kare kambunsa a gasar 2017 a London
2016-12-07 19:59:18 cri
Zakaran wasan kwallon kafan nan na tseren mita 800 dan asalin kasar Kenya David Rudisha baya samun hutu a sakamakon yunkurin da yake yi na kokarin kare kambunsa a gasar da za'a gudanar a shekarar badi ta kwararru a London.

Rudisha, mai shekaru 28, ya bayyana cewa, yana kokarin maida hankali ne a gasar ta London kuma baya son samun cikas game da gasar wasannin da za'a gudanar ta Olympics a Tokyo a shekarar 2020.

Yace "mun shirya ni da kociya na Bro Colm, kuma mun cimma matsaya guda. Abinda yafi muhimmanci a yanzu shine yadda zamu tsara hanyar da zan cigaba da rike kambuna a gasar wasannin. Ina son na lashe gasar a kakar wasanni ta 2017"

Rudisha, wanda ya koma kasar bayan wani rangadi da ya gudanar a kasar Amurka da Turai, yace ya fara wani kwarya-kwayar samun horo, kuma zai koma kasar Australiya a watan Fabrairun shekarar 2017 domin shiga gasar.

Yace "ina tunanin akwai abubuwa da dama dake gabana kuma ina yin nazari game da yadda zan bullowa al'amarin. Zan kasance mai gaskiya, akwai abubuwa masu yawa da zamu gudanar tare da kociya na bayan an dawo daga hutun bikin kirsimeti. Mun tattauna game da gasar wasannin Olympic ta 2020, to sai dai muna gudanar da shirye shirye a kowace shekara".

Yace "zamantowa zakara abune mai kyau, amma lashe gasar wasannin Olympic sau 3 babban al'amari ne. Ya danganta da yadda naji jikina ke motsawa, kuma idan naji karfin jiki sosai a cikin shekaru 4, zan iya shiga gasar. A lokacin zan kasance ina da shekaru 33 a duniya, kuma duk da haka wadan nan shekaru babu matsala game da shiga gasar. Zan saurara naji yadda jikina zai bayyana mini".

Shidai Rudisha, ya samu raunuka ne a lokacin gasar wasannin Olympic ta shekarar 2012, kuma ya fara jin karfin jikinsa a shekara guda data gabata. Amma wannan matsalar ta kara matsa masa kaimi na kokarin ganin ya cigaba da rike matsayinsa a gasar wasannin Olympic ta 2017 kuma yana fata shekarar ta kasance mai matukar muhimmanci a fagen sana'arsa.

Shidai zakaran wasan tseren mita 800 na duniyar, yana son ya kafa tarihi ne a duniya ta yadda za'a dinga tunawa da shi bisa irin nasarorin da ya cimma a rayuwa. (Ahmad Fagam)

Rudisha yace "har yanzu akwai jan aiki a gaba. Usain Bolt ya yi nasarar lashe lambobin yabo na zinare har sau 3 a jere a gasar wasannin Olympic. A gasar tseren mita 800, babu wanda ya taba samun lambar yabo har sau 3 a jere. Wannan babban abu ne mai kara kwarin gwiwa".

" Ina sauraron shekarar 2020. Ina da kyakkyawan tsammani idan har na warke, na kuma sami koshin lafiya, da kuma kyakkyawan horo, to hakan zai kara mini kwarin gwiwa".

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China