in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunawa da 'yan wasan da muka yi rashinsu a 2016
2017-01-05 20:49:09 cri

 

Ban da wannan kuma, a nan kasar Sin, wani tsohon mai horas da 'yan wasan kwallon kafa Zeng Xuelin ya kwanta dama a ranar 11 ga watan Fabrairun wannan shekara. Ana iya tunawa da tsohon dan wasan kwallon kafan ne bisa irin salon shugabancinsa, a loakcin da ya jagoranci babbar tawagar kwallon kafan kasar a wasannin cin kofin nahiyar Asiya a shekarar 1984.

Haka zalika, a lokacin da tawagar 'yan wasan kwallon kafan ta Sin ta kwashi kashinta a hannun takwararta ta yankin Hong Kong, a wasansu a shekarar 1985, lamarin ya haifar da rashin baiwa kasar damar shiga gasar cin kofin duniya a shekarar 1986, batun da ya bakantawa hukumar wasannin kasar Sin rai, hakan ya sa daga bisani marigayi Zeng yayi murabus daga mukaminsa.

1 2 3 4 5 6 7 8 9
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China