To,ban da wannan tsohon kociyan kasar Sin kuma, kar mu manta, wasu daga cikin kwararrun da suka ba da babbar gudumowa ga cigaban harkokin wasanni na duniya sun rasu a shekarar 2016.
Cikinsu akwai kwararren dan jaridar nan mai gabatar da rahoton wasanni na kasar Sin Gao Dianmin, wanda ya gabatar da jerin rahotannin wasannin Olympics na lokacin zafi tun daga shekarar 1984 zuwa ta 2016. Ya rasu a sakamakon bugun zuciya a ranar 11 ga watan Nuwamba yana da shekaru 62 a duniya. Gao shi ne dan jarida na farko a duniya da ya fara watsa labari game da nasarar da Xu Haifeng ya samu a matsayin dan wasan kasar Sin na farko da ya fara lashe lambar yabo ta zinare a wasnnin Olympics, lambar da ya samu a wajen Olympics na shekarar 1984 a birnin Los Angeles na kasar Amurka.
Xu Haifeng, shahararren dan wasan harbi na kasar Sin ya taba magana kan halayyar Gao, inda ya ce ,"yana da saukin kai kuma yana da kyakkyawan hali, tun kafin lokacin shahararsa dama bayan ya shahara. Ko menene ya faru, ba ya ta da hankalinsa. Shi kyakkyawan abin koyi ne ga matasan 'yan jarida."
Gao, ya jima a matsayin mamba na kwamitin 'yan jaridu na kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC, ya fara aiki da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a 1977 bayan ya kammala karatun jami'a. Gao ya halarci wasannin Olympics na Beijing da London da kuma na Rio. Wanda zai kasance abin koyi ga matasan 'yan jaridu dake dauko rahoton wasanni a kasar Sin.