in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunawa da 'yan wasan da muka yi rashinsu a 2016
2017-01-05 20:49:09 cri

To, ban da Gao na kasar Sin, sunan "Silvio Gazzaniga" ba wani sananne ba ne a duniya, to amma sunansa ya bar wani abin ga tarihi da za'a dade ana tunawa.

Kofin lambar yabo da hukumar wasannin kwallon kafa ta duniya wato FIFA take amfani da shi a matsayin babbar kyautar da ake baiwa zakaran gasar cin kofin duniya, Gazzaniga ne ya tsara shi. Mutumin dan asalin kasar Italiya ne, an haife shi a shekarar 1921 kuma ya mutu a ranar 31 ga watan Oktoban 2016. An zabi zanensa ne daga cikin nau'ikan zane 53 na lambobin yabon, mai tsayin centimeter 36.8, wanda aka kera shi da zinaren nau'in carat 18 wanda ke da nauyin kilo 6.17.

Duk kungiyar wasan kwallon kafan da ta yi nasara ana rubuta sunanta a wani bangare na kofin. Kuma akwai isassun wuraren da za'a ci gaba da zayyanawa har zuwa gasar cin kofin duniya ta shekarar 2038.

1 2 3 4 5 6 7 8 9
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China