A daya bangaren kuma tsohon dan wasan kwallon kafa kuma shahararren koci Johan Cruyff shi ma ya rasu a ranar 24 ga watan Maris yana da shekaru 69 a duniya bayan ya sha fama da ciwon daji.
Ana dai danganta irin ci gaban da kungiyar kwallon kafar Barcelona ta Sifaniya ta samu a Turai da ma sauran gasannin duniya da irin gudummawar da koci Cruyff ya baiwa kungiyar, lokacin da yake horas da ita.
Cruyff na cikin rukunin manyan 'yan kwallon duniya kamar su Pele na Brazil da Diego Maradona da Franz Beckenbauer. Shi ne kuma na farko cikin wadannan 'yan wasa da ya rasu. Wannan koci ya kafa tarihi wajen horas da manyan kungiyoyin kwallon kafa kamar su Ajax, da FC Barcelona da ma kungiyar kasa ta Sifaniya.