Sa'an nan, daya daga cikin munanan ibtila'in da suka faru a harkar wasanni a duniya a cikin shekarar 2016 shi ne na kudancin Amurka. A yayin da jirgin saman dake dauke da 'yan wasan kwallon kafa na Chapecoense daga kasar Brazil ya yi hadari a Colombiya a ranar 28 ga watan Nuwamba. 'Yan wasan 19 sun mutu, lamarin da ya haifar da kaduwa ga tawagogin 'yan wasan kwallon kafa dake yankin na kudancin Amurka gami da daukacin al'ummar kasashen duniya baki daya.
Ko da yake tawagar 'yan wasan, wato kulob din Chapecoense, ba wata sananniya ba ce, amma dai Chapecoense tana yunkurin yin fice a duniya daga yankin kudancin Amurkan. Kungiyar wasan tana kan hanyarta ne don halartar wasan karshe na cin kofin kwallon kafa na kudancin Amurka (wato Copa Sudamericana a Turance).
Domin nuna karamci da girmamawa ga kungiyar Chapecoense, abokiyar karawarta Atletico Nacional ta bukaci hukumar shirya wasannin kwallon kafa ta kudancin Amurka (conmebol) data ayyana takwararta a matsayin wacce ta lashe gasar cin kofin kwararru ta kudancin Amurka ta 2016.