161222-wurin-ibada-da-ya-shahara-a-fannin-wasa-kunfu-Bello.m4a
|
Idan an nazarci tarihin wurin ibadar Shaolin, za a gano cewa wuri ne mai tarihi sosai. An ce tun shekara ta 490, wani sufi dan kasar Indiya mai suna Ba Tuo ya zo kasar Sin don yada addinin Buddah, inda sarkin Sin a lokacin ya tarbe shi da hannu biyu-biyu, ya kuma taimake shi wajen kafa wurin ibadar Shaolin a kan wani dutse mai suna Songshan.