in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunawa da 'yan wasan da muka yi rashinsu a 2016
2017-01-05 20:49:09 cri

Har wa yau shi ma tsohon shugaban hukumar FIFA Joao Havelange ya rasu yayin gasar Olympics ta shekarar 2016 wanda ya gudana a birnin Rio de Janeiron kasar Brazil. Havelange ya rasu ne yana da shekaru 100 bayan da kasar sa ta dauki nauyin wannan shahararriyar gasa.

Havelange ya jagoranci FIFA tsawon shekaru 24 tsakanin shekarun 1974 zuwa 1998. Ya kuma gabatar da sauye sauye da dama a hukumar ta FIFA, matakin da ya bunkasa hada hadar kasuwanci a hukumar.

Havelange ya taka gagarumar rawa wajen tabbatar da nasarar da Brazil ta samu wajen daukar nauyin gasar Olympic ta 2016, da ma gasar cin kofin duniya na shekarar 2014. Burin Havelange na ganin birnin sa na Rio ya karbi bakuncin gasar Olympic cikin nasara ya sanya shi ci gaba da kazar kazar a shekarar 2009 lokacin yana da shekaru 93, har dai ta kai shi ga cimma wannan buri kafin rasuwar sa.

1 2 3 4 5 6 7 8 9
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China