Cikin wani bayanin gargadi da ofishin ya fitar, ya ce akwai matukar yiyuwar 'yan ta'adda za su kaddamar da harin ta'addanci a Afirka ta Kudu, ko da yake ba a iya tabbatar da inda za su kaiwa harin ba, amma mai iyuwa ne ya zamo a wasu wuraren saye da sayarwa, inda baki 'yan kasashen waje kan kai ziyara a birnin Johannesburg ko Cape Town.
Haka kuma, bayanin ya ce a halin yanzu, 'yan kasar Birtaniya na fuskantar karin kalubalen ta'addanci, sakamakon rikice-rikicen dake aukuwa a kasashen Iraqi da Syria, don haka ya kamata a kara mai da hankali kan wannan lamari.
Dangane da wannan batu, ministan tsaron kasar Afirka ta Kudu David Mahlobo, ya bayyana a jiya Litinin cewa, hukumomin tsaron kasarsa za su ci gaba da yaki da masu tsattsauran ra'ayi, da 'yan ta'adda, a wani mataki na tabbatar da tsaron rayukan al'ummar kasar. (Maryam)