Jaridun Star, da Pretoria News, da Cape Times da sauransu wadanda kamfanin yada labarai na "Freedom" dake kasar Afirka ta Kudu ke mallakarsu, sun gabatar da wannan bayani, inda aka furta cewa, Sin tana da ikon mallakar tsibiran tekun kudu, wanda hakan ke da cikakkun shaidun tarihi.
Har wa yau kasar Sin tana kokarin gudanar da shawarwari da wadannan kasashe na yankin tekun kudu dake yunkurin samun ikon mallakar tsibiran a wannan yanki, tare da fidda ra'ayinta na raya tsibirai tare da su, shi ya sa aka tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudu na Sin.
Dadin dadawa, bayanin ya ce, Amurka ce ta yi magudi kan wannan batu a boye. A cikin shekarun baya da suka wuce, sabo da gwamnatin Amurka dake karkashin jagorancin Barack Obama tana bin tsarin 'Sake samun daidaito a nahiyar Asiya da tekun Pasifik', shi ya sa yanayin da ake ciki a yankin tekun kudun ke kara tsananta.(Fatima)