in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya bukaci kasashen duniya su dakile tsattsauran ra'ayin nuna karfin tuwo bisa ma'auni guda
2016-04-09 13:44:33 cri

Jakadan kasar Sin kuma zaunannen wakilin kasar Sin dake birnin Geneva Ma Zhaoxu, ya jaddada bukatar kasahen duniya su dunkule wuri guda don yakar laifuffukan tsattsauran ra'ayin nuna karfin tuwo a duniya kuma bisa ma'auni daya.

Zhaoxu, ya furta hakan ne a wajen babban taro kan batun rigakafin tsattsauran ra'ayin nuna karfin tuwo da aka gudanar a birnin Geneva.

Ya kara da cewa, dole ne a kawar da tsattsauran ra'ayin nuna karfin tuwo, wanda ke haifar da ta'addanci a duniya baki daya.

Batun tsattsauran ra'ayin nuna karfin tuwo ya zama babbar barazana ga duk kasashen duniya, ya kamata kasashen duniyar su yi aiki tare don cimma wannan buri.

Kasar Sin ta bukaci MDD da kwamitin sulhu ba da jagoranci wajen hada kan membobi kasahen majalisar, don daukar matakai da suka dace. Sa'an nan, dole ne su bi ma'auni guda wajen yakar nau'o'in ayyukan ta'addanci.

Bugu da kari, Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, kasar Sin ita ma tana fama da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi. Kungiyar Turkestan ta Gabas tana yada tsattsauran ra'ayi da ta'addanci da aikata laifuffukan ta'addanci, wadda ta kawo barazana sosai ga tsaron kasar Sin. Kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace, domin yaki da tarzoma da masu tsattsauran ra'ayi, da kuma yin hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya bisa tsarin MDD, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China