Shugaban ya fadi haka ne yayin wani taron gangamin magoya bayan jam'iyyar ANC wanda aka shirya a filin wasan FNB dake birnin Johannesburg domin kaddamar da zabukan 'yan majalisun da za a gudanar a jihar Gauteng ta kasar. A cewar shugaban, yadda hukumar Standard & Poor (S&P) mai nuna matsayin tattalin arzikin kasashe daban daban ta yanke shawarar kiyaye matsayin kasar maimakon saukar da shi, ya nuna cewa za a iya farfado da tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu, idan jama'ar kasar za su yi hadin gwiwa tare.
Kafin haka kuma, Standard & Poor (S&P) ta sanar da matsayin kudaden kasar Afirka ta Kudu a ranar Jumma'a, inda ta kiyaye matsayin maimakon saukar da shi zuwa wani yanayin lalacewa.(Bello Wang)