in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomi da kwararru na ECOWAS na goyon bayan nagartattun tsare tsare domin magance annobar ta'addanci
2016-05-21 17:29:25 cri
Hukumomi da kwararru da suka fito daga kasashe mambobin kungiyar ECOWAS sun shawarci a ranar Jumma'a a birnin Abidjan na Cote d'Ivoire game da bullo da nagartattun tsare tsare ta yadda za a yaki ta'addanci da magance annobar a shiyyar.

Hukumomi da kwararru da suka yi wani zaman taro a babban birnin tattalin arzikin Cote d'Ivoire game da yarjejeniyar da ta shafi kasuwancin makamai a yankin ECOWAS a karkashin jagorancin ma'aikatar harkokin wajen Cote d'Ivoire, sun nuna cewa ya dace a gudanar da manyan ayyukan a cikin yanayin da duniya take ciki na fuskantar sabbin barazana ta fuskar tsaron kasa da kasa.

Hadin gwiwar ayyuka da kokari sun zama dole domin yaki da yaduwar makamai, da yaki da barazanar tsaro, musamman ma ta'addanci, in ji wakilin ma'aikatar harkokin wajen Cote d'Ivoire, Ladji Meite.

A cewarsa, moriya da kalubalolin dake da nasaba da kula da sanyo ido kan makamai na misaltuwa da halin munanan tashe tashen hankali na makamai da asarar rayuka dalilin yin amfani da wuce kima da wadannan makamai.

A lokuta da dama, hukumomi da kwararrun yammacin Afrika sun bayyana cewa ta'addanci na kasancewa babbar barazana ga shiyyar kuma ya zama dole a dauki matakan fuskantar wannan batu.

A nasa bangare, shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara, ya bayyana baya bayan nan cewa kasarsa ta dukufa ka'in da na'in wajen yaki da ta'addanci, tare kuma da tabbatar da cewa kasarsa za ta cigaba da aiki tare da gamayyar kasa da kasa domin magance annobar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China