Kudurin da 'yan jam'iyyar hamayyar Afrika ta Kudu suka gabatar a majalisar dokokin kasar game da neman tsige shugaba Jacob Zuma daga mukaminsa ya gamu da tutsu, bayan da 'yan hamayyar suka gaza samun rinjaye kan kudurin a yayin kada kuri'a a jiya Talata.
Mahawarar ta haifar da rudani, yayin da 'yan hamayyar suka fice daga zauren majalisar bayan sun gaza samun nasara kan kudurin.
'Yan majalisar 233 ne suka kada kuri'ar kin amincewa da kudurin, yayin da takwarorinsu dake son tsige Zuma su 143 ne.
Jam'iyyar ANC ta shugaba Zuma ce ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar.
Wannan mataki ya biyo bayan shari'ar da wata babbar kotun kasar ta yi ne a makon jiya, game da zargin da ake wa Shugaba Zuma na karkatar da akalar makudan kudaden gwamnati don bukata ta kashin kansa na gyaran wani katafaren gidansa dake kauyensu.
Mmusi Maimane, shi ne shugaban jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance (DA) ya ce, har yanzu ba su hakura ba kan wannan aniya.
Ya ce, jam'iyyar adawar za ta rubuta wasika ga shugaban majalisar dokokin kasar Baleka Mbete, domin ba su dama ta ladaftar da mista Zuma.
'Yan adawar kasar sun jima suna zargin shugaba Zuma da aikata laifukan rashawa da rashin iya mulki, lamarin da ya haifar da cece-kuce tsakanin 'yan adawar da 'yan jam'iyyar mai mulki a majalisar dokokin. (Ahmad)