A sa'i daya kuma, ya yi fatan nasarar gudanar zaben gwamnatocin kanannan hukumomin na watan Agustan dake tafe cikin kyakkyawan yanayi.
An dai yi wa taron addu'ar lakabi da "ranar addu'ar hadin gwiwa, da zaman lafiya, da samun ruwan sama, da kuma cimma nasarar zabukan gwamnatocin kanannan hukumomin kasar". Har wa yau kuma, Mr. Zuma ya ce, wani muhimmin dalilin da ya sa aka gudanar da wannan taro na addu'a a Afirka ta Kudu shi ne, hada kan 'yan kasar baki daya, duba da bambancin addinai da suke da shi, wanda hakan zai ba da gudummawa wajen dunkulewar su.
Shugaba Zuma tare da shugabannin 'yan kasuwa, da jami'an lardin Natal, da ministan harkokin raya zamantakewar al'ummar kasar, da magajin garin, da wasu shugabannin addinai a kasar, duka sun halarci wannan taro.
Cikin jawabin da ya gabatar yayin taron, shugaba Zuma ya ce, babban takensa shi ne hade fannoni daban daban, kamar na zaman lafiya, da hadin gwiwa, da gina kasar, ciki had da inganta zamantakewar al'umma wadda za ta kawar da nuna bambanci a tsakanin maza da mata da sauran kabilu daban daban dake Afirka ta Kudu. Ya kara da cewa, ba za a yafe wa duk wadanda aka kama na aikata laifuka masu alaka da ta da hankula a kasar ba. (Maryam)