Sanarwar ta jaddada niyyar yaki da ta'addanci ta hanyar hadin gwiwa, da yin Allah wadai da duk wane irin ta'addanci, kana taron ya bayyana ra'ayin kasashe membobin kungiyar na ci gaba da yin hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci.
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana a gun taron manema labaru bayan kammala taron cewa, ta'addanci ya fi kawo babbar illa ga kasashen mulsumi.
Shugaba Erdoğan ya sanar a ranar 14 ga wata cewa, kasashe membobin kungiyar OIC sun amince da shawarar da Turkiya ta bayar game da kafa cibiyar hadin gwiwa ta 'yan sanda ta kungiyar OIC a birnin Istanbul, wadda za ta kasance tsarin hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci da sauran manyan laifuffuka.
Game da halin da ake ciki a kasar Syria, sanarwar ta jaddada nuna goyon baya ga warware batun ta hanyar siyasa bisa tushen sanarwar Geneva, kana ta nuna goyon baya ga MDD da ta jagoranci wannan yunkuri.
Za a gudanar da taron kungiyar OIC na gaba a birnin Banjul na kasar Gambia, ko da yake ba a tsaida lokacin gudanar da shi ba. (Zainab)