Shugaba Jacob Zuma ya yi Allah wadai da ta da hargitsi da wasu mutane suka yi game da nuna adawa da shata kan iyakoki a garin Vuwani da ke lardin Limpopo.
Baki daya kasar na cikin yanayi na rudani sakamakon tashin hankalin da ya barke, lamarin da ya haddasa kone makarantun gwamnati kimanin 17 da wasu gine-ginen gwamnati, Zuma ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mai da martani game da kuri'ar da majalisar dokokin kasar ta kada game da kasafin kudi.
Shugaba Zuma ya bayyana hakan ne a yayin da rikicin ya shiga rana ta 4 a garin Vuwani.
An ruwaito cewa, mazauna garin Vuwani sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna adawa da matakin da hukumar shata kan iyakoki ta kasar ta dauka na mayar da garin karkashin ikon kwaryar babban birnin kasar.
Zuma ya ce, bai san irin kalaman da zai yi amfani da su ba domin nuna bacin ransa, sakamakon lalata makarantun da aka yi wadanda aka gina su ne domin taimakawa al'umma masu tasowa a nan gaba a garin Vuwani domin yaki da talauci, da matsalar rashin aikin yi da samar da daidaito.
A cewar Shugaban, tuni gwamnatin ta ba da umarni ga hukumomin tsaro domin bankado wadanda ke da hannu domin hukunta su. (Ahmad)