in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boma-bomai sun fashe a kusa da ofishin magajin birnin Mogadishu
2016-04-12 10:44:15 cri
A ran 11 ga wata, wasu boma-boman da aka dasa cikin wata mota sun fashe a wani wurin dake kusa da ofishin magajin birnin Mogadishu na kasar Somaliya, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla guda biyar, yayin da 7 suka jikkata.

Bisa labarin da aka samu, an ce, wata mota dake dauke boma-bomai ta kutsa kai kan bangon dake kusa da ofishin magajin birnin Mogadishu, sa'an nan, motar ta fashe, lamarin da ya haddasa mutuwar fararen hula guda biyar. Amma, ya zuwa yanzu, babu wanda ko wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin harin din.

Kwanan baya, sojojin kungiyar AU da rundunar sojojin tsaron kasar Somaliya sun karfafa matakan soja kan kungiyar Al-Shabaab, lamarin da ya haddasa mai da martanin kungiyar kansu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China