Kwamitin sulhun MDD ya gudanar da taro game da batun yankin Sahel, inda cikin jawabin da ya gabatar, Wu Haitao ya ce kamata ya yi kasashen duniya su dora muhimmanci kan babbar illar da ayyukan ta'addanci suke haifarwa a yankin Sahel, da kara zuba jari ga yankin don yaki da ta'addanci.
Wu Haitao ya kara da cewa, Sin da Afirka suna da buri iri daya, da moriya ta bai daya. Kana kasar Sin tana fatan ci gaba da kokari tare da kasashen Afirka, don gudanar da ayyukan da za su amfani nahiyar Afirka, ciki har da kasashen yankin na Sahel. Ta hakan ne kuma za a cimma burin samun zaman lafiya da wadata, da kuma bunkasuwa a nahiyar Afirka. (Zainab)