An fara gudanar da taron masu neman daidaitawa na kungiyar G20 karo na biyu ne daga ranar 6 zuwa ranar 8 ga wannan watan Afrilu a birnin Guangzhou na kasar Sin, a matsayinta na kasar da za ta karbi bakuncin wannnan taro, kasar Sin ta yi kira ga mambobin kasashen kungiyar G20 da su ba da wata sanarwar shugaba kan batun sauyin yanayi, domin sa kaimi ga mambobin da su aiwatar da ayyukan da abin ya shafa bisa yarjejeniyar Paris yadda ya kamata, haka kuma, ta yi kira ga mambobin da su kulla yarjejeniyar a ranar 22 ga watan Afrilu, ko kuma a lokacin baya cikin sauri, sa'an nan su shiga yarjejeniyar bisa manufofinsu yadda ya kamata, domin a fara aiwatar da yarjejeniyar cikin sauri.
Haka kuma a yayin taron, da aka gudanar a birnin Guangzhou, dukkan bangarori masu ruwa da tsaki sun tattauna kan sanarwar, sa'an nan, sun cimma matsaya guda.
Bugu da kari, bangarorin sun nuna yabo matuka kan kokari da jagorancin da kasar Sin ta yi a yayin taron, inda a cewarsu, sanarwar ta nuna aniyar kungiyar G20 wajen aiwatar da yarjejeniyar Paris yadda ya kamata, sannan za ta kara hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa game da daidiata sauyin yanayi. (Maryam)