A sakon da ya aika, firaministan ya ce, za a gudanar da taron kolin kungiyar a wannan shekara a birnin Hangzhou na kasar ta Sin. Kamata ya yi kasashe mambobin kungiyar su kara daidaitawa da juna a fannin tsara manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, a yayin da suke tsara manufofin tattalin arziki nasu, ya kamata su yi la'akari da tasirin da ka iya haifar ga sauran kasashe, don a kiyaye kwanciyar hankalin kasuwannin hada-hadar kudi a duniya. Sa'an nan, ya kamata a sa kaimin gyare-gyaren tsarin tattalin arziki, don samar da kuzari ga bunkasuwar tattalin arziki. Na uku, ya kamata a kyautata aikin kula da harkokin tattalin arziki da hada-hadar kudi a duniya, don kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai adalci a duniya.(Lubabatu)