A gun bikin bude taron, ministan kudi na Sin, Lou Jiwei ya bayyana cewa, taron zai share fagen taron kolin kungiyar da za a shirya a Hangzhou ta fannin hada hadar kudi, tare da yin shawarwari kan yanayin tattalin arzikin duniya, da karuwarsa, da manufofin da kasa da kasa ke bi wajen farfado da tattalin arziki da sauransu.
Kafin bude taron kuma, shugaban bankin duniya, Kim Yong ya bayyana cewa, ko da yake saurin karuwar tattalin arziki ya ragu, amma Sin tana kokarin yin jerin kwaskwarima ga tsarin tattalin arzikinta, kamar sa kaimi ga kiyaye muhalli da neman samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da sa kaimi ga samar da sabbin fasahohi, da raya tarbiya bisa iyakacin kokari da sauransu, wadanda za su samar da kuzari ga bunkasuwar tattalin arziki. Ba shakka, dukkan wadannan matakai za su sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin Sin zuwa wani sabon mataki.(Fatima)