in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da a fuskanci kalubalen sauyin yanayi
2016-03-24 13:57:02 cri
A jiya Laraba 23 ga watan ne babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, ya gabatar da jawabi game da ranar hasashen yanayi ta kasa da kasa, inda ya yi kira ga gamayyar kasashen duniya da su dauki matakai yadda ya kamata, na fuskantar kalubalen sauyin yanayi, da kuma samun dauwamammen ci gaba.

A watan Yuni na shekarar 1960 ne, kungiyar hasashen yanayi ta kasa da kasa, ta zartas da kudurin sanya ranar 23 ga watan Maris na ko wace shekara, ya zamo ranar hasashen yanayi ta kasa da kasa.

Babban taken ranar hasashen yanayi na shekarar bana shi ne, fuskantar kalubalen samun karuwar zafi, da karin fari, da kuma karin ambaliyar ruwa a gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China