A yayin bikin, mataimakin ministan harkokin cinikayya na kasar Sin Wang Shouwen ya yi jawabin fatan alheri, inda ya ce, yanzu tattalin arzikin duniya ya shiga tangal-tangal, kuma a cikin shekaru 4 da suka gabata, saurin bunkasuwar cinikayyar duniya ya yi kasa da saurin bunkasuwar tattalin arziki, kuma abun da ya kawo tsaiko game da bunkasuwar tattalin arziki, ya kamata kungiyar kasashen G20 su lalubo bakin zaren warware batun.
Mista Wang ya ce, a gun taro karo na farko da aka yi a karshen watan Janairu a birnin Beijing, Sin ta gabatar da shawarar kafa tsarin G20 , da sa kaimi ga raya cinikayyar kasa da kasa, da nuna goyon baya game da tsarin cinikayyar bangarorin daban daban, da sa kaimi ga hadin gwiwa da shawarwari game da manufofin saka jari a duniya, da sa kaimi game da samun ci gaba a duniya, abun da ya samu amincewar bangarorin daban daban a duniya. Kasar Sin tana sa ran yin kokari tare da kasashen duniya, don samun sakamako mai gamsarwa a wadannan fannoni, kuma za a mika su a yayin taron ministocin cinikayya na G20 da taron koli na Hangzhou da za a yi a watan Satumban bana.(Bako)