in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a tsara ayyukan dake gaban kome da ka'idoji yayin da ake yin kwaskwarima kan tsarin G20
2016-02-26 14:14:50 cri
Ministan harkokin kudi na kasar Sin Lou Jiwei ya bayyana a birnin Shanghai a yau Jumma'a 26 ga wata cewa, a halin yanzu, an kasa yin kwaskwarima kan tsarin G20 bisa zaton da ake yi, kamata ya yi a kara yin kokarin tsara ayyukan dake gaban kome da ka'idoji da kuma kafa tsarin yin nazari.

Lou Jiwei ya bayyana hakan ne a gun taron tattaunawa kan kwaskwarimar tsarin G20 a wannan rana.

Game da kwaskwarimar tsarin, Lou Jiwei ya bayyana cewa, ya kamata a sa kaimi ga yin ciniki da zuba jari, da yin kwaskwarima kan kasuwar kwadago, da samar da ayyukan yi, da kara zuba jari a fannin ilmi, da kara yin kirkire-kirkire da kuma tabbatar da samar da kudi wajen samun bunkasuwa mai dorewa.

Ban da wannan kuma, za a maida fannonin raya ayyukan more rayuwa, kiyaye muhalli da kuma yin kwaskwarima kan hada-hadar kudi a matakin gaba yayin da ake yin kwaskwarima kan tsarin G20. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China