in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
G20 ta alkawarta daukar matakan gaggauta domin farfadowar tattalin arzikin duniya
2016-02-28 12:40:12 cri
Kungiyar kasashe ashirin masu karfin tattalin arziki a duniya wato G20, ta bayyana aniyar tallafawa farfadowar tattalin arzikin duniya, ta hanyar aiwatar da manufofin kudi da na tsare-tsaren gwamnatoci.

Hakan dai na kunshe ne cikin takardar bayan taro da mahalarta taron kungiyar suka fitar jiya a birnin Shanghai na nan kasar Sin. Sanarwar ta bayyana cewa duk da cewa tattalin arzikin duniya na kara farfadowa, a hannu guda ba a samu cikakken daidaito game da farfadowar tasa ba, don haka kungiyar ke fatan amfani da dabaru daban daban don ganin an magance wannan matsala.

Mahalarta taron da suka kunshi ministocin kudi da gwamnonin manyan bankunan kasashe mambobin kungiyar, sun bayyana cewa manufofin gwamnatoci masu nagarta da suke fatan aiwatarwa, za su karfafa ci gaba, tare da samar da karin guraben ayyukan yi, baya ga karfafa gwiwar sassan tattalin arzikin duniya. Taron dai na yini biyu ya zo ne a gabar da ake fama da koma bayan tattalin arzikin duniya, da kuma rashin tabbas a kasuwannin kudi.

A farkon wannan mako ne asusun bada lamuni na IMF, ya bayyana irin rashin tabbas da farfadowar tattalin arzikin duniya ke fuskanta, yana mai kira da a dauki karin matakai na kaucewa karin koma baya. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China