in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da bikin fara nuna wasan kwaiwayon Sin da harshen Larabci da bidiyon "Sannu, Sin" a kasar Masar
2016-01-21 11:20:09 cri

A daren jiya Laraba 20 ga wata ne, aka gudanar da bikin fara nuna wasan kwaikwayon Sin mai taken "soyayyar mahaifa" , wanda aka fassara shi zuwa harshen Larabci, da kuma bidiyon "Sannu, Sin" a kasar Masar.

Cikin jawabin da shugaban hukumar kula da ayyukan watsa labaru, da wallafa littattafai, da harkokin redio, telebijin, da fina-finai ta kasar Sin, mista Cai Fuchao ya gabatar a gun bikin, ya ce an fara nuna wasan kwaikwayon na Sin mai taken "soyayyar mahaifa" wanda aka fassara shi zuwa Larabci, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyara a kasar Masar, tare da kaddamar da bukukuwan shekarar al'adun Sin da Masar, da kuma taya murnar cika shekaru 60 da kulla dangankatar diplomasiyya a tsakanin Sin da Masar.

Ya ce a halin yanzu, Sin da Masar suna da ra'ayi daya kan manya tsare-tsare da manufofin raya kasa, don haka kamata ya yi wasan kwaikwayo da shirye-shiryen rediyo na kasashen biyu, su sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kara fahimtar juna a tsakanin jama'arsu.

A nasa bangare, shugaban kawancen rediyo da telebijin na kasar Masar Essam Amir, cewa yayi a shekarun baya baya nan, Masar da Sin sun yi hadin gwiwa sosai a fannin ayyukan rediyo da telebijin, kuma yadda aka nuna wasan kwaikwayo na "soyayyar mahaifa" daya ne daga cikin nasarorin hadin gwiwar su. Ya yi nuni da cewa, Sin da Masar su ne kasashe mafiya tarin al'adu a gabashin duniya, kana suna fuskantar matsalolin zamantakewar al'umma kusan iri daya. Don haka, yana sa ran ganin wasan kwaikwayo na kasar Sin zai samu karbuwa sosai a kasar Masar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China