Ministan raya al'adun kasar Masar Helmy al-Namnam, ya shedawa kamafanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, bikin raya al'adun na shekara-shekara zai kara dankon zumunta dake tsakanin kasashen biyu.
Wannan sanarwa ta zo ne a yayin taron manema labaru a birnin Alkahira na kasar .
An sanya shekarar 2016 a matsayin shekarar mai armashi ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ne tun a yayin wata ganawa tsakanin shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar a watan Disambar shekarar 2014 a birnin Beijing.
Masar ita ce kasa ta farko a kasashen Larabawa a nahiyar Afrika da ta fara amincewa da kasar Sin.
A nasa bangaren minista mai kula da ofishin jakadancin kasar Sin a Masar Qi Qianjin, ya ce dangantakar dake tsakanin Sin da Masar tana kara samun bunkasuwa ne a kullum.
Qi ya kara da cewar, Masar ita ce kasar da ta fara kafa cibiyar raya al'adun Sinawa a kasarta, sannan ita ce kasar da ta hada Sin da sauran kasashen Larabawa.(Ahmad Fagam)