in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya taya murnar ranar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Masar
2016-01-20 19:30:31 cri
A yayin da shugaban kasar Sin yake ziyara a kasar Masar, mujallar Larabci ta China Today ta kebe wani shafi na musamman kan ranar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Masar, inda kuma aka yi bikin sayar da mujallar a birnin Alkahira, hedkwatar Masar. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Masar Abdel-Fattah el- Sisi sun yi jawabi a dangane da wannan batu

A jawabinsa, shugaba Xi ya furta cewa, Sin da Masar suna da dogon tarihi. Tun asali, jama'arsu suna sada zumunci tsakaninsu bisa hanyar Siliki. Masar ke kasa ta farko da ta kulla huldar diplimasiyya da Sin a cikin kasashen Larabawa dake nahiyar Afirka. A cikin shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, ana raya dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata, har ma sun zama abin koyi a fannin yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.

Bayan haka, shugaba Xi ya ce, a shekarar 2014, an daga matsayin dangantakar da ke tsakaninsu zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare a dukan fannoni. Sin na fatan hada kai tare da Masar domin sada zumunci, da koyon darasi daga wajen juna, da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu ta hanyar shirin nan na "Ziri daya da hanya daya", domin kara kawo alheri ga jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangare, shugaban Masar Abdel-Fattah el-Sisi ya furta cewa, yana maraba da zuwan shugaba Xi kasar Masar. Kuma Masar tana darajanta dangantakar da ke tsakaninta da Sin. Tana kuma fatan za a ci gaba da raya wannan dangantaka a dukkan fannoni. (Fatima Liu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China