Cikin sanarwar, an bayyana cewa, a wannan rana, jiragen saman sojan kasar sun kai hare-hare kan wurare guda hudu na kungiyar IS dake arewacin kasar Iraqi, inda, sojojin suka lalata sansanonin kungiyar guda hudu a yankin, sai dai ba a bayyana adadin rasuwa da jikkatar mutane sakamakon hare-haren ba.
Bugu da kari, an ce, a ran 26 ga wata, dakarun kungiyar IS sun kai farmaki a wani sansanin horaswa na sojojin kasar Turkiya a birnin Mosul dake arewacin kasar Iraqi, lamarin da ya haddasa rasuwar sojan kasar Turkiya guda daya, da jikkata guda. (Maryam)