A taron da suka yi a birnin Paris, ministocin tsaron kasashen Faransa, Amurka, Australia, Jamus, Ingila, Italiya da Netherlands sun tabbatar da kudurin su na karfafa farmakin su a kan kungiyar ta IS domin samar da gaggarumin nasara mai dorewa a kan kungiyar.
A cikin sanarwar bayan taro, mahalarta taron sun yi nuni da bukatar dake akwai na cigaba da kara karfi wajen yakin su da kungiyar IS tare da shirya matakin gaba da za'a yi amfani da shi domin dakushi karfin kungiyar.
Manyan hafsoshin sojin kasashen guda 7 sun kuma amince da yin nazarin ayyukan da suke yi a kai a kai da duba cigaban da aka samu.
A taron manema labarai da suka yi gaba dayan su tare da babban hafsan tsaron kasar Amurka Ashton Carter, da ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drain sun ce kungiyar IS suna ja da baya saboda an samu nasarar lallata kayyayakin su, don haka yanzu lokaci yayi na kara azama gaba daya ta hanyar aiwatar da wani sabon dabara ta soji.(Fatimah Jibril)