Shugaba Erdogon jim kadan kafin ya tashi daga birnin Istanbul zuwa kasar Saudiya don ziyarar aiki ya furta cewa ba yadda za'a yi a ce an goyi bayan gwamnatin kasar da ta hallaka jama'ar ta da ba su ci ba ba su sha ba har sama da 400,000 da makamai na zamani da ma masu guba.
Har ila yau ya zargi wassu kasashen da kara rura wutan rikici ta goyon bayan jam'iyyar demokradia na tarayyar Kurdawa wato PYD na kasar Syriya da kuma bangaren masu dauke da makamai na jam'iyyar YPG.
Kasar Turkiya tana daukan dukkan wadannan jam'iyyu biyu a matsayin na 'yan ta'adda saboda alakar su da tsohuwar jam'iyyar ma'aikata ta Kurdawa wato PKK na kasar ta, abin da ya sa take nuna fargaban zasu iya kafa jihar kurdawa mai cin gashin kanta a arewacin Syria.
Shugaba Erdogab yace kau da ido a kan kisan kare dangi na kungiyoyin 'yan ta'adda kamar su PYD da YPG, don kawai sun ce suna fafutuka ne a kan dakile Daesh wato sunan kungiyar IS da larabci, ya zama rura wutan rikici.
Amurka da Rasha gaba dayan su suna goyon bayan kungiyoyin biyu, saboda ana daukan su a matsayin wadanda suka cancanta wajen yakar kungiyar IS.(Fatimah)