in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Amurka sun kama wani masanin kera makamai masu guba na IS
2016-03-10 13:23:12 cri
Jami'an rundunar sojan kasar Amurka sun tabbatar a jiya cewa, kwanan baya, sojojin kasar Amurka sun kama da wani masanin makamai masu guba na kungiyar IS Sreiman Al Afari inda suke yi masa tambayoyi. Bayanan da masanin ya bayar, ya taimakawa sojojin wajen lalata wuraren ajiye makamai masu guda na kungiyar IS da dama dake kasar Iraqi.

Rahotanin da kafofin yada labarai na Amurka da dama suka bayar ya bayyana cewa, jami'an rundunar sojan kasar Amurka sun tabbatar cewa, a watan gabata ne rundunar sojoji ta musamman ta kasar Amurka ta kama Sreiman Al Afari a yayin da suke gudanar da ayyukansu a arewacin kasar Iraqi. Kuma wannan shi ne karo na farko da sojojin Amurka suka tabbatar da damke wani dan kungiyar IS.

Bugu da kari, an ce, Sreiman Al Afari dan kasar Iraqi ne, wanda ya taba aiki a gwamnatin Saddam Hussein, ya kuma kware a harhada makamai masu guba da na kwayoyin halitta.

Kafin kamun nasa, Sreiman Al Afari shi ne shugaban reshen kungiyar IS dake kula da harkokin makamai masu guba, yana da bayanai masu muhimmanci game da adadin makamai masu guba da sauran bayanai game da abin ya shafa.

A halin yanzu kuma, sojojin Amurka suna tsare da shi a sansaninta dake birnin Erbil na kasar Iraqi, kaza lika,a wannan makon ne sojojin Amurka ke shirya kammala sauraron kara, daga bisani su mika shi ga gwamnatin kasar Iraqi.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China