Duk da hakan basu sanar da wani matakin mai kamar hakan ba da zasu dauka a kasar Libya domin hana ayyukan soji na kungiyar ta IS kara yawaita.
Babban taron na ministocin kasashe 23 ministan harkokin wajen kasar Italiya Paolo Gentiloni ne tare da Ministan harkokin wajen Amurka John Kerry suka jagoranta tare.
A jawabin shi Mr Gentiloni yace ana samun cigaba akan kungiyar ta IS ko kuma Daesh, amma kungiyar da ake fuskanta na da dabaru kwarai da shirin da bai kamata a dauka da wasa ba.
Ministocin 23 a takardar bayan taron sun ce zasu inganta kokarin su tare da gaggauta fadakarwa akan kungiyar a Iraqi da Syriyan. Yana mai bayyana kudurinsu na tunkarar kungiyar kai tsaye tare da rage tasirin kungiyar a duniya.
Sai dai kuma Ministocin basu bayyana matakin soja na kai tsaye a kasar Libyan dake arewacin African ba a nan gaba kadan.
Sanarwar ta ce suna biye tare da damuwa akan karuwar karfin kungiyar ta IS ko Daesh a Libya kuma zasu ci gaba da sa ido sosai a wajen. Kuma zasu tsaya cikin shiri na taimakama gwamnatin hadaka na Libyan domin samar da zaman lafiya da tsaro ma al'ummar ta.