in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da hare-haren boma-bomai a babban birnin Turkiya
2016-03-14 10:58:08 cri

Wani hari da aka kaddamar da boma-bomai a wata tashar Bas dake Guven, wani wurin shakatawa dake birnin Ankara na kasar Turkiyya, ya yi sanadiyyar rasuwar mutane a kalla 34, tare da jikkatar wasu mutanen 125, ciki hadda wasu 19 dake cikin mawuyacin hali.

Rahotanni na cewa yayin harin na daren jiya Lahadi, maharan sun shake wata mota ne da boma-bomai, sannan suka tarwatsa motar, lamarin da ya haifar da mummunan sakamako. Tuni dai 'yan sanda suka killace wurin da harin ya auku, domin fara bincike.

Ya zuwa yanzu, 'yan sanda sun riga sun gano lambar injin motar da aka dasa boma-baman cikin ta, sa'an nan suna ci gaba da binciken asalin motar.

Bugu da kari, an ce, a yayin da harin ya auku, 'yan sanda dake dandalin Red Crescent na musayar aiki, don haka ake zaton burin maharan shi ne yiwa 'yan sandan kwantan bauna. Kaza lika, an ce mai iyuwa ne, magoya bayan kungiyar 'yan adawar PKK ne suka shirya kaddamar da harin.

Dama dai cikin watanni biyar da suka gabata, an kai makamancin wadannan hare-haren ta'addanci masu tsanani har sau uku, a babban binin kasar ta Turkiya wato Ankara. 'Yan kasar dai na nuna bacin rai game da matakan da gwamnati ke dauka, da na kungiyoyi masu leken asirin kasar, inda suke kira ga gwamnatin kasar da ta dauki matakan gaggawa yadda ya kamata, domin damke wadanda suka shirya irin wadannan hare-hare, tare da dakile sake aukuwar su a nan gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China