Reshen IS dake Yemen, ya sanar da hakan ne a wata sanarwa a shafukanta na sada zumunta, inda ta nuna cewar mai kai harin ya fito ne daga kasar Netherland domin kaddamar da harin bam a birnin Aden.
Kusan sojoji 10 dake gadin shugaban kasar harin ya hallaka, ciki harda manyan jami'an fadar shugaban kasar, sannan wasu karin jami'an 20 suka jikkata a lokacin kaddamar da harin, a cewar sanarwar.
Da ma dai kungiyar IS ta sha barazanar kaddamar da hare hare kan shugaban kasar Yemen wanda kasashen duniya suka amince da shi Abdu-Rabbu Mansour Hadi da kuma gwamnatinsa
Masana a kasar ta Yeme sun bayyana cewar, wannan shine karon farko da reshen kungiyar IS dake Yemen ya dauko hayar mahara daga kasashen yammacin duniya don kaddamar da hare hare a Yemen.(Ahmad Fagam)