Mr Carter ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, inda ya ce, yanzu sojojin kasar Amurka na kokarin kawar da manyan shugabannin kungiyar IS bisa shirin, rasuwar Abu Ala Afri zai gurgunta ayyukan da kungiyar ke gudanarwa a kasashen Iraki da Syria da kuma yankunan dake dab da su.
Amma, Carter bai fayyace wurin da aka dauki matakin a kai ba, da kuma hanyar da sojojin Amurka suka dauka na aiwatarwa.
CNN ya ruwaito maganar wani jami'in ma'aikatar tsaron kasar Amurka da ya bukaci a sakaya sunansa na cewa, sojojin Amurka ta yi shirin kama Abu Ala Afri, amma sojojin musamman dake wata jirgin sama mai saukar ungulu sun canja shirin,suka kuma harbe motar dake daukar Abu Ala Afri. Labarin dai bai bayyana dalilin da ya sa aka canja shirin da wurin da aka aikata aikin ba. (Bilkisu)