Kungiyar ta yi wannan kiran ne a taron ministocin harkokin waje da ta kira jiya Alhamis a birnin Alkhahiran Masar.
Babban sakataren kungiyar Nabil al-Araby ya ce abin da kasar Turkiyan ta aikata tamkar keta dokokin kasa da kasa ne.
Ko da ya ke kasar Turkiyan ta sanar da cewa, ta fara janye dakarunta daga yankuan kasar ta Iraki sakamakon kiran da shugaban Amurka Barack Obama ya yi wa kasar Turkiya da ta janye dakarun nata. Amma ministan harkokin wajen kasar Iraki ya nace cewa, abin da suke bukata shi ne Turkiya ta gaggauta janyewa a aikace ba wai maganar fatar baki ba.
A farkon watan Disamba ne kasar Turkiya ta jigbe dakarunta a wani sansanin da ke kasar ta Iraki da sunan shirin samar da horo a yakin da ta ke yi da kungiyar IS.(Ibrahim)