in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai sauran bangarorin da suke da hannun yin fashewar bom a Istanbul, a cewar firaministan Turkiya
2016-01-14 11:01:31 cri
Firaministan kasar Turkiya Ahmet Davutoğlu ya bayyana cewa, 'yan sandan kasar Turkiya sun kama mutane 4 da ake zarginsu da hannu a harin bam din da aka kai birnin Istanbul, kana suna bincike don gano ko akwai sauran wadanda da hannu a harin da aka kai.

Davutoğlu ya bayyana wa 'yan jarida bayan da ya shugabanci wani taron tsaro a birnin Istanbul a wannan rana cewa, kungiyar IS kungiya ce da ta kai harin,amma akwai wasu dake bayanta. A cewar jami'in, wasu kasashe suna kokarin ganin sun cusa kasar Turkiya a cikin rikice-rikice,a saboda haka kasar Turkiya tana kokarin zakulo wadanda suka tsara wannan hari.

Bayanai na nuna cewa,a wannan rana bayan fashewar bam din, 'yan sandan kasar Turkiya sun kama mutane 60 da ake zargi da hannu cikin kai harin, ciki har da 'yan kasar Rasha guda uku. Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Rasha suka bayar, an ce, 'yan sandan kasar Turkiya sun kama 'yan Rashan uku ne a cikin gidajensu, inda suka samu wasu takardu da dama. 'Yan sanda na ganin cewa, wadannan mutane uku suna taimakawa ayyukan ta'addanci.

Harin na birnin Istambul ya haddasa mutuwar Jamusawa 10 tare da raunatar wasu 'yan kasashen waje 17. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China